IQNA

Sakon Da Gasar Kur'ani Shi Ne Karfafa 'Yan Uwantakar Musulmi

23:53 - July 14, 2010
Lambar Labari: 1956050
Bangaren kasa da kasa; Babban sakon da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ke isarwa shi ne samara da hadin kai da fahimtar juna gami da karfafa dangantaka tsakanin al'ummar musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi da daya daga cikin mahalarta gasar karatun kur'ani da ake gudanarwa a birnin Tehran daga kasar India Sayyid Sulaiman ya bayyana cewa, babban sakon da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ke isarwa shi ne samara da hadin kai da fahimtar juna gami da karfafa dangantaka tsakanin al'ummar musulmi na duniya baki daya, duk da irin banbamce-banbancen da ke tsakaninsu.

Bayanin ya ci gaba da cewa makarancin ya karfafa wajabcin samun fahimtar juna da kuma yi juna kyakkyawan zato tsakanin dukkanin bangarori na al'ummar musulmi a fadin duniya baki daya.

613292



captcha