Bangaren kasa da kasa; Mabiya mazhabar shi'a a kasar Pakistan sun gudanar da wani zaman taro a birnin Islam-abad, inda suka tattauna kisan da aka yi wa wasu 'yan uwansu a cikin wannan wata da muke ciki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani bayani daga shafin sadarwa na yanar gizo na shites news cewa, mabiya mazhabar shi'a a kasar Pakistan sun gudanar da wani zaman taro a birnin Islam-abad, inda suka tattauna kisan da aka yi wa wasu 'yan uwansu a cikin wannan wata da muke ciki na shamsiyya.
Taron ya nuna rashin gamsuwa da irin matakan da wasu masu tsattsauran ra'ayin kafirta musulmi suke dauke kan mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah a kasar, inda suka bayyana hakan da cewa ya saba wa dukknin koyarwa irin ta addinin musulunci.
A bangare guda kuma sun dora wa mahukuntan kasar Pakistan laifin rashin daukar kwararan matakai na ba su kariya daga barazanar 'yan ta'adda da suke samun karfin gwiwa daga wasu kasashen larabawa masu akidar wahabiyanci.
613592