Bangaren kas ada kasa; An kammala wani taro kan finafinan palastinawa da aka gudanar a kasar Turkiya, wanda ma'aikatar kula da harkokin yawon bude ido ta kasar ta dauki nauyin shiryawa tare da gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na star cewa, an kammala wani taro kan finafinan palastinawa da aka gudanar a kasar Turkiya, wanda ma'aikatar kula da harkokin yawon bude ido ta kasar ta dauki nauyin shiryawa tare da gudanarwa a kasar.
Wanda ya jagoranci gudanar da wannan shiri Umar Sharkawi ya bayyana cewa muhimman abubuwa da ake fatar cimmawa daga gabatar da irin wadannan fina-finan ita ce, bayyana halin da al'ummar palastinu suke ciki, da kuma irincin da suke fuskanta daga haramtacciyar kasar Isra'ila.
613592