Bangaren kasa da kasa; Gasar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa na ci gaba da gudana a birnin Tehran, inda mahalarta gasar ke gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan yadda ake gudanar da ita da kuma banbamcinta wasu irinta a wasu kasashen.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa day a gudanar da daya daaga cikin mahalarta gasar da ake gudanarwa a birnin Tehran daga kasar Gyrgystan Zomabek ya bayyana cewa, gasar ta sha bamban da wadda ya halarta a birnin Moscow na kasar Rasha, inda ya ce wadda yake halarta a halin yanzu tafi ba shi sha'wa.
Ya ce yana fatan a kowace shekara ya kasance daya gada cikin wadanda za su samu damar halartar gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a da ake gudanarwa a jamhuriyar musulunci ta Iran.
612779