IQNA

An Fitar Nushar Kur'ani Ta Digital Ga Makafi A Kasar Masar

20:37 - July 15, 2010
Lambar Labari: 1956236
Bangaren kasa da kasa; An samar da nushar kur'ani mai tsarki ta hanyar digital domin amfanin makafi da kuma masu matsalar gani a babban dakin karatu na birnin Iskandariya da ke kasar Masar.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga jaridar misriyun da ake bugaw a akasar Masar an bayyana cewa, an samar da nushar kur'ani mai tsarki ta hanyar digital domin amfanin makafi da kuma masu matsalar gani a babban dakin karatu na birnin Iskandariya da ke kasar Masar, wanda kuma za a iya yin amfani da na'ura mai kwakwalwa wajen karanta wannan nusha.

Bayanin ya kara da cewa yanzhu haka ana shirin samar da irin wannan na'ura domin amfanar makafi da masu matsalar gani a kasashen musulmi, ta yadda ba za a barsu a baya ba wajen karatun kur'ani mai tsarki.

613307


captcha