Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran Cihan ya habarta a shafinsa na yanar gizo cewa, ma'ikatar kula da harkokin addini a Cyprus ta kudu da ke karkashin ikon Turkiya ta yi Allawadai da kai harin da wasu mutane suka yi kan ajujuwan koyar da addini a bangaren da ke karkashin ikon kasar Girka a cikin Tsibirin.
Bayanin ya ci gaba da cewa wasu daga cikin masu tsattsauran ra'ayin kiyayya da musulmi ne suka shirya kai wannan hari kan ajujuwan musulmi masu koyon karatun kur'ani mai tsarki a yankin.
Yanzhu haka dai bayanan da malaman addini gami da cibiyar kula da harkokin addini ta bangaren tsibirin da ke karkashin mulkin Turkiya suka fitar, ya sanya ana tunanin fara gudanar da bincike kan lamarin.
614239