A wata zanatawa da ta hada kamfanin dillancin labaran iqna da daya daga cikin alkalan da suka gudanar da alkalanci a gasar kur'ani ta duniya da aka gudanar a Iran Farajallah Mahmud Shazili, wanda ya zo daga kasar Masar ya bayyana cewa, makarancin kur'ani mai tsarki dan kasar Iran Masud Nikdasti ya taka rawar gani a gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa da aka gudanar a birnin Tehran, fadar mulkin kasar Iran.
Ya ce duk da cewa makarancin na kasar Iran ana gudanar da wannan gasa a cikin kasarsu ne, amma babu mai shakku kan cewa ya yi karatu yadda ya kamata, ya kuma burge dukkanin mahalarta gasar da suka zo daga kasashen duniya daban-daban.
614293