Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, majiyoyin bangaren kula da hulda da jama'a na cibiyar Imam Ali (AS) da ke birnin Vienna ta habarta cewa, za a gudanar da tarukan addini na cikin watan sha'aban abirnin Vienna na kasar Austria, wanda babbar cibiyar nan mai kula da harkokin addinin Musulunci a kasar za ta dauki nauyin shirya tare da gudanarwa a birnin.
Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka an fara gudanar da irin wadannan taruka, inda a jiya aka gabatar da jawabai kan zagayowar ranar haihuwar Imam Hussain (AS) a babban ginin cibiyar, tare da halartar daruruwan musulmi.
614433