Kamfanin dillacin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na internet haber an bayyana cewa, bisa sabbin dokokin da majalisar dokokin kasar Turkiya ta amince da su za a rufe duk shafukan yanar gizo masu cin zarafin addinin Musulunci da sauran addinai a kasar ta Turkiya.
Rahoton ya ce wannan dokar ta bayar da dama ga ma'aikatar da ke kula da harkokin addini a kasar da ta sanya ido kan dukkanin shafukuka, domin rufe duk wani shafin yanar gizo da ke cin zarafin addinin Musulunci.
Wannan doka dai 'yan majalisar dokokin kasar ne suka amince da ita tare da bayar da umurni da ta fara aiki nan take ba tare da wani bata lokaci ba.
614490