Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin sadarwa na iba'a an habarta cewa, An kammala gudanar da wani zaman taro da ya yi bahasi kan nazariyar nan ta mahdawiyya da ke bincike kan hakikanin Imam Mahdi (AS) wanda aka gudanar a birnin Moscow fadar mulkin kasar Rasha, taron da ya samu halartar masana daga sassa na kasar.
Rahoton ya kara da cewa wadanda suka halarci zaman taron sun mayar da hankali ne kan ra'ayoyin da aka kawo dangane da bayyanar Imam Hamdi, kama daga bangaren mahangar shi'a da kuam mahangar 'yan sunna.
Daga cikin mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah da suka halarci zaman taron sun kawo dalilai daidai da mahangar mazhabar ja'afariyya kan Imam Mahdi (AS)
615336