IQNA

Makaranta Iraniyawa Sun Bayar Da Abin Koyi A Gasar Kur'ani

18:33 - July 17, 2010
Lambar Labari: 1957276
Bangaren kasa da kasa; Daya daga cikin makaranta kur'ani mai tsarki na kasar Jordan da ya halarci gasar kur'ani ta kasa da kasa da aka gudanar a birnin Tehran ya bayyana cewa, makaranta Iraniyawa sun bayar da kyakkyawan misali da sauran makaranta.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zanatawa da ta hada shi da Abdulrahman Muhammad Ali daya daga cikin makaranta kur'ani mai tsarki na kasar Jordan da ya halarci gasar kur'ani ta kasa da kasa da aka gudanar a birnin Tehran ya bayyana cewa, makaranta Iraniyawa sun bayar da kyakkyawan misali da sauran makaranta da suka halarci gasar daga wasu kasashen musulmi.

Ya ce daga fitattun makaranta kur'ani na duniya da suka hada da Muhammad Sadiq Minshawi da kuma Ragib Mustafa Galwash, duk sun yaba da yadda makaranta Iraniya suka nuna kwazo da himma a wajen karatun.

615304



captcha