IQNA

Za A kafa Wani Kwamitin Kare Masallcin Qods Mai Alfarma

18:34 - July 17, 2010
Lambar Labari: 1957277
Bangaren kasa da kasa; Za a kafa wani babban kwamiti na kasa da kasa domin kare masallacin qods mai alfarma, wanda zai hada mambobi daga kasashen musulmi na duniya.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran sana an habarta cewa, za a kafa wani babban kwamiti na kasa da kasa domin kare masallacin qods mai alfarma, wanda zai hada mambobi daga kasashen musulmi na duniya da ma wadanda ba na musulmi ba.

Babbar manufar kafa wannan kwamiti ita ce bin diddigin lamurran da suke faruwa a birnin Qods da kuma irin matakan da haramtacciyar kasar Isra'la take dauka na takura wa palastinawa, da kuma keta alfarmar masallaci gami da sauran wurare masu tsarki da take yi.

615255



captcha