Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga jaridar khaleej times an habarta cewa, a cikin watan Ramadan mai zuwa za a gudanar da wasu shirye-shirye da suka danganci karatun kur'ani da harda da dai sauran abubuwan da suka danganci kura'ni mai tsarki a birnin Dubai na kasar hadaddiyar daular larabawa a cikin masallatan birnin.
Ma'aikatar kula da ayyukan addini ta kasar ce za ta dauki nauyin shiryawa tare da gudanar da wannan shiri. Yanzu haka dai an kammala dukkanin abubuwan da za a yi, wajen aiwatar da wannan shiri a cikin Ramadan mai zuwa.
615676