Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa; a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nun an bayyana cewa, wakilai daga kasashen duniya ne suka halarci taron maulidin Imam hussain (AS) da aka gudanar a birnin karbala mai alfarma an kasar Iraki. Bayanin ya ci gaba da cewa daga cikin kasashen da suka halarci taron har da Canada, Newziland, Faransa, Sweden, Masar, Oman, Morocco, Algeria, India, Kuwait, Senegal, Turkiya, Ghana, Jamus, Pakistan, kamaru, Tunisia, Bahrain, Iran, Syria, Lebanon, Birtaniya gami da wakilai na sauran kungiyoyi gami da mazhabobi na kasar Iraki.
Babbar manufar gudanar da taron maulidin dai ita ce kara karfafa dankon zumuntaka tsakanin dukkanin bangarori na addinin Musulunci, ba tare da nuna wani bangaranci ko abin da ya yi kama da haka ba.
615590