IQNA

Dan Majalisar Holland Mai Gaba Da Musulunci Zai Kafa Wata Kungiya

17:32 - July 18, 2010
Lambar Labari: 1957975
Bangaren kasa da kasa; Dan majalisar dokokin nan na kasar Holland mai tsananin gaba da addinin Musulunci na shirin kafa wata kungiya da zata dukkanin kungiyoyi masu tsananin gaba da addinin Musulunci a duniya.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na cnnturk an habarta cewa, dan majalisar dokokin nan na kasar Holland mai tsananin gaba da addinin Musulunci na shirin kafa wata kungiya da zata dukkanin kungiyoyi masu tsananin gaba da addinin Musulunci.

Bayanin ay ci gaba da cewa dan majalisar mai suna Geert Wilders ya shahara wajen bayyana addinin Musulunci a mtsayin mafi muni daga cikin addinai, ta hanyar fitar da bayanai da kuma fina-fina na kyamar Musulunci.

615695










captcha