Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto da aka watsa a shafin sadarwa na yanar gizo na interfaith cewa, za a fara gudanar da wani shiri na bayar da horo kan ilmomin addinin Musulunci a kasar Newziland da nufi kara fadada fahimta da koyarawa irin ta addinin Musulunci a kasar, wanda shi ne karo na biyu da za a gudanar da irin wannan shirin a kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa babbar ciyar yada ilmomi da al'adun Musulunci ta kasar Newziland mai suna Rashid ita ce ta dauki nauyin gudanar da wannan shiri, wanda zai samu halartar wakilai daga sassa daban-daban na kasar.
615597