Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da tarukan maulidin Imam Hussain (AS) a birnin London na kasar Birtaniya a cikin wannan wata, wanda babbar cibiyar kula da harkokin addinin Musulunci ta birnin za ta dauki nauyin shiryawa tare da gudanarwa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ic-el an bayyana cewa, za a gudanar da tarukan maulidin Imam Hussain (AS) a birnin London na kasar Birtaniya a cikin wannan wata, wanda babbar cibiyar kula da harkokin addinin Musulunci ta birnin za ta dauki nauyin shiryawa tare da gudanarwa a cikin wannan wata.
Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka an kallama dukkanin shirye-shiryen da suka kamata domin gudanar da wannan shiri, mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah a birnin London da ma sauran sassa na kasar Birtaniya suna saba gudanar da irin wadannan shirye-shirye.
Daga cikin muhimman abubuwan da za a gudanar a wajen taron maulidin na Imam Hussain (AS) akwai karatun kur'ani mai tsarki, sai kuma laccoci dam asana gami da malamai za su gabatar.
615554