Cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna bayan ta nakalto daga majiyar labarai ta Muzin ta watsa rahoton cewa; Rafi'I Amiri shugaban mu'assisar Kur'ani a kasar Iraki ya ce sun kuduri aniyar ganin sun bawa hardar kur'ani muhimmanci fiye da wani abu a wannan shekara. Rafi'I ya bayyana hakan ne alokacin wata tattaunawa da ta hada shi da cibiyar inda ya yi bayani dalla dalla kuma a takaice kan yadda yin haka ked a matukar muhimmanci da kuma dalilin da ya sa suka dauki wannan mataki. Kuma wannan ya z one a daidai lokacin da yake tare da tawagar mahardata da makaranta kur'ani mai girma na Iraki a gasar karatun kur'ani da aka gudanar ta kasa da kasa karo na ashirin da bakwai a nan birnin Tehran na jamhuriyar Musulunci ta Iran.
616507