IQNA

Ana Ci Gaba Da Buga Littafan Addini Na Kananan Yara A Jamus

16:47 - July 19, 2010
Lambar Labari: 1958690
Bangaren kasa da kasa; ana ci gaba da buga littafan addinin Musulunci domin amfanin kananan yara a kasar Jamus, wanda cibiyar buda littafai ta salam take daukar nauyin yi da nufin karfafa gwiwar yara wajen koyon ilmomin addinin Musulunci.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa mosque-strasbourg cewa, ana ci gaba da buga littafan addinin Musulunci domin amfanin kananan yara a kasar Jamus, wanda cibiyar buda littafai ta salam take daukar nauyin yi da nufin karfafa gwiwar yara wajen koyon ilmomin addinin Musulunci tare da ilmomin sanin zamantakewar rayuwa.

Bayanin ya kara da cewa yanzu haka ana sayar da littafan a cikin farashi mai sauki, ta yadda iyayen yara musulmi za su yin amfani da su wajen tarbiyantar da yaransu, da kuma koyar da su muhimman ilmomi da ya kamata su sani a cikin addinin Musulunci.

616826



captcha