Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na umma-united cewa, Za a gudanar da wani zaman taro a birnin Bordaford na kasar Birtaniya domin yin bahasi kan shakhsiyyar manzon Allah (SAW) da sakon da yake dauke da shi ga dukkanin 'yan adam a fadin duniya.
Bayanin ya kara da cewa taron zai mayar da hankali wajen yin dubi ga matsayin manzon Allah (SAW) da kuma yadda ya kasance mai son adalci kuma aikata shi a aikace a cikin rayuwarsa, gami da gaskiyarsa da kuma wajabcin sonsa.
616610