IQNA

Rubutun Makaloli A Gasar Kur'ani Ta Tehran Ya Yi Gagarumin Tasiri

16:41 - July 19, 2010
Lambar Labari: 1958695
Bangaren kasa da kasa; Rubutun makalolin da aka yi a lokacin gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Tehran, ya yi gagarumin tasiri wajen kara wa juna sani kan bangarori daban-daban da suka danganci muhimmancin gasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi da daya daga cikin mahalarta gasar kur'ani ta birnin Tehran daga palastinu Ala'uddin Ayyubi, ya bayyana cewa rubutun makalolin da aka yi a lokacin gudanar da gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Tehran, ya yi gagarumin tasiri wajen kara wa juna sani kan bangarori daban-daban da suka danganci muhimmancin gasar kur'ani mai tsarki.

Ya kara da cewa an kafa kwamitoci da dama a lokacin gudanar da gasar kur'ani ta birnin Tehran, wadanda suka mayar da hankali wajen ganin an gudanar da dukkanin bangarorin gasar kamar yadda aka shirya.

Haka nan kuma ya bayyana gasar da cewa tana daya daga cikin muhimmai irinta da aka gudanar a duniya da ya samu halarta, kamar yadda ya yabawa jami'an Iran wajen mayar da hanakali kan lamurran kur'ani da suke yi.

616685





captcha