IQNA

Lauyoyi Daga Kasashen Duniya 36 Za Su Kai Karar Isra'ila

16:49 - July 19, 2010
Lambar Labari: 1958697
Bangaren kasa da kasa; Lauyoyi daga kasashen duniya da adadinsu ya kai mutane satin daga kasashen duniya talatin da shida, suna shirin kai karar Haramtacciyar kasar Isra'ila a gaban kuliya dangane da ta'addancin da take tafkawa.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin sadarwa na resalehaber ya habarta a shafinsa na yanar gizo cewa, lauyoyi daga kasashen duniya da adadinsu ya kai mutane satin daga kasashen duniya talatin da shida, suna shirin kai karar Haramtacciyar kasar Isra'ila a gaban kuliya dangane da ta'addancin da take tafkawa akan al'ummar palastinu da sauran al'ummomin duniya.

Lauyoyin wadanda suka fito daga kasashen Turkiya da ma wasu kasashen na daban, za su mayar da hankali a karar tasu kan harin ta'addancin da haramtacciyar kasar Isra'ila ta kai kan jirgin ruwan nan mai dauke d atimako zuwa ga al'ummar Gaza, inda ta kashe mutane tara daga cikin masu kai agajin.

616614





captcha