Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da jaridar alraya ta kasar Qatar ta watsa a shafinta na yanar gizo an bayyana cewa, babbar cibiyar kula da ayyukan kur'ani ta kasar Qatar tana shirin fara aiwatar da wani shiri na yawan shakatawa bisa manufofi na addinin Musulunci a kasar da sauran kasashen musulmi da na laraba.
Bayanin ya ci gaba da cewa babbar manufar kirkiro da wannan shiri ita ce samar da wata hanya ta yawan bude ido domin sanin muhimman wurare na tarihin Musulunci, da ke cikin kasashen musulmi da na larabawa, gami da lamurra da suka danganci ilimi da ake ta kara samun ci gaba a kansu a addinin Musulunci, wanda ganin hakan zai kara karfafa gwiwar musulmi.
616558