IQNA

Za A Gudanar Da Taron Harkokin Kasuwancin Musulmi A Malazia

16:51 - July 20, 2010
Lambar Labari: 1959406
Bangaren kasa da kasa; Za a gudanar da wani babban taro na kasa da kasa kan harkokin kasuwanci da suka hada kasashen musulmi, wanda za a gudanar babban dakin gudanar da taruka na jami'ar Malaya da ke birnin Kualalampour.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na sahirnews cewa, Za a gudanar da wani babban taro na kasa da kasa kan harkokin kasuwanci da suka hada kasashen musulmi, wanda za a gudanar babban dakin gudanar da taruka na jami'ar Malaya da ke birnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malazia.

Rahoton ya ci gaba da cewa wannan taro da za a gudanar a cikin watan gobe, zai mayar da hanakali ne wajen tattauna muhimamn batutuwa da suka danganci harkokin kasuwanci na kasa da kasa tsakanin kasashen musulmi.

Daga ciki kuwa har da batun saka hannayen jari a manyan kamfanoni da kanana na kasashen musulmi, ko kuma mallakin musulmi da suke cikin wasu kasashen.

617306










captcha