Kamfanin dillanicin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran saba na gwamnatin kasar Yeman an bayyana cewa, an fara gudanar da gasar hardar kur'ani mai ta matasa a matsayi na kasa baki daya a kasar Yeman, wadda ke samun halartar matasa daga sassa daban-daban na kasar baki daya.
Rahoton ya ci gaba da cewa wannan shi ne karo na hudu da ake gudanar da irin wannan gasar kur'ani a kasar. An kasa yanayin yadda ake gudanar da ita zuwa kashi hudu, bisa la'akari da matsayin hardar da matasan suke da ita.
Sama da yara talatin n eke cikin gasar wadanda suka hardace kur'ani mai tsarki baki daya, amma ana sa ran mataki na karshe za a fitar da wadanda suka yi nasarar lashe dukkanin bangarori ne.
617240