Bangaren kasa da kasa; Bayar da lamba kan kira'ar tangimi ga masu gudanar da gasar hardar kur'ani ba adalci ba ne a gasar kur'ani ta kasa da kasa da aka gudanar a Iran, domin hakan yana danne hakkokin wasu mahardata.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da hada shi da daya daga cikin mahalarta gasar kur'ani da aka gudanar a birnin Tehran da yazo daga kasar Syria Umar Nazir ya bayayna cewa, bayar da lamba kan kira'ar tangimi ga masu gudanar da gasar hardar kur'ani ba adalci ba ne a gasar kur'ani ta kasa da kasa da aka gudanar a Iran, domin hakan yana danne hakkokin wasu mahardata.
Ya ci gaba da cewa bayar da lambar da aka yi ga wadanda suke yi karatu da kira'a ta tangimi a cikin gasar harda ya sabawa ka'idojin harda, kuma yin haka rashin adalci nega sauran mahardata da ba su bin salon tangimi a cikin karatu, kuma suna karatun daidai da ka'ida.
Ya bukaci da a dauki matakan gyara a nan gaba a sauran tarukan gasar kur'ani da za a gudanar a Iran da sauran kasashen musulmi da aka egudanar da ita a matsayi na kasa da kasa.
617488