Bangaren kasa da kasa; Mambobin kungiyoyin musulmi na yankin Cataloni na kasar Spain sun gudanar da babban zamansu a birnin Bercelona, inda suka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi harkokin musulmi a kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ucide an habarta cewa, mambobin kungiyoyin musulmi na yankin Cataloni na kasar Spain sun gudanar da babban zamansu a birnin Bercelona, inda suka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi harkokin musulmi a kasar ta Spain baki daya.
Bayanin ya yi nuni da irin himmar da kungiyoyin musulmin kasar Spain suke da ita wajen yada manufofin addinin Musulunci a kasar, tare da fahimtar da sauran mutane da ba musulmi sanin hakikanin manufofin addinin Musulunci da koyarwarsa, musamman ma kan batutuwa da suka danganci rayuwar jamam'a ta zamantakewa.
617474