Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na na yanar gizo na vicmusulmis an habarta cewa, za a gudanar da gasar hardar kur'ani mai tsarki da ta kebanci mata a kasar New Zeland, wadda za a fara gudanarwa daga ranar 16 ga watan Mordad na wannan shekara.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan gasar hardar kur'ani kwamitin musulmi na jami'ar birnin Victoria ne ya shirya ta, kuma an kasa bangarorin da za a gudanar da gasar daidai da adadin mahardatan da kuma bangarorin da za su gudanar da gasar hardar a cikinsu.
Akwai wadanda za su gudanar da ta su gasar a bangaren farko na kur'ani, wato daga juzu'I na farko har zuwa juzu'I na biyar, daga nan kuma akwai wadanda daga na farko ne har zuwa na goma sha biyar, da kuma daga farko zuwa na talatin abin da ya yi sama.
617253