IQNA

An Kirayi Musulmin Kasar Malazia Da Su Hada Kansu

15:11 - July 21, 2010
Lambar Labari: 1960080
Bangaren kasa da kasa; Mai bayar da shawarwari na musamman kan harkokin addinin Musulunci ga fira ministan kasar Malazia Datuk AbdullahAamadi Zain, ya kirayi dukkanin musulmin kasar da su bayar da muhimmanci wajen samun hadin kansu baki daya.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na BERNAMA an habarta cewa, babban mai bayar da shawarwari na musamman kan harkokin addinin Musulunci ga fira ministan kasar Malazia Datuk AbdullahAamadi Zain, ya kirayi dukkanin musulmin kasar da su bayar da muhimmanci wajen samun hadin kansu baki daya duk kuwa da banbancin fahimta kan wasu lamurra.

Rahoton ya kara cewa mai bayar da shawar ga fira ministan ya tabbatar da cewa hadin kai tsakanin al'ummar musulmi shi ne babban sirrin duk wata nasara a cikin lamurransu, kuma sai sun hada kai ne za su iya yin tasiri a cikin sauran al'ummomi.

618212


captcha