Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran iba ya habarta a shafinsa na sadarwa cewa, kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasar Saudiyya suna ci gaba da sukar lamitrin gwamnatin kasar kan ci gaba da kame mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah tare da takura musu da take yi ba gaira ba sabar.
Bayanin kungiyoyin ya tabbatar da cewa yanzu haka mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah da dama da suke tsare ba tare da sun aikata wani laifi ba, kuma ba gurfanar da su a gaban kuliya domin sanar da su dalilin kame su ba.
Masana kan harkokin dan adam suna kallon irin wannan mummunan aikin da gwamnatin wahabiyawan saudiyya ke aikatawa kan mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah a matsayin wani babban laifin nuna wariya da banbanci ga wasu jama'ar kasar.
618150