Bangaren kasa da kasa; Kungiyar bayar da agaji ta musulmin kasar Amurka ta samu yabo a matsayi na kasa da kasa, inda aka bayyana ta a matsayin kungiyar bayar da agaji da ta fi taka gagarumar rawa a wannan shekara, kamar yadda ta zo a wanan matsayi shekaru bakwai a jere.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin sadarwa na yanar gizo na prnewswire cewa, kungiyar bayar da agaji ta musulmin kasar Amurka ta samu yabo a matsayi na kasa da kasa, inda aka bayyana ta a matsayin kungiyar bayar da agaji da ta fi taka gagarumar rawa a wannan shekara, kamar yadda ta zo a wanan matsayi shekaru bakwai a jere tare da samun lambar yabo ta duniya.
Kungiyar bayar da agaji ta musulmin Amurka tana taka gagarumar rawa wajen taimaka ma mutane da suke bukatar taimako a ko'ina cikin fadin duniya, tare gudanar da ayyuka na hadin gwiwa da sauran kungiyoyi na kasa da kasa.
Wannan kungiya dai tana samun kudaden shiga ne daga irin gudunmawar da su kansu musulmin kasar Amurka suke bayarwa ne, da nufin gudanar da ayyuka na jin kai ga musulmi da ma wadanda ba musulmi ba.
618189