IQNA

Makaranta Kur'ani Iraniyawa Sun Yi Fice A Duniyar Musulmi

15:21 - July 21, 2010
Lambar Labari: 1960091
Bangaren kasa da kasa; Samun matsayi na daya da makarancin kur'ani dan kasar Iran Masud Nidasti ya yi a gasar kur'ani ta kasa da kasa da aka gudanar ya tabbatar da cewa makaranta Iraniyawa sun samu shuhura.


A wata zantawa da kamfanin dillancin labaran iqna ya gudanar da wani makarancin kur'ani mai tsarki dan kasar Sri lanka Jamil Muhammad ya bayyana cewa, samun matsayi na daya da makarancin kur'ani dan kasar Iran Masud Nidasti ya yi a gasar kur'ani ta kasa da kasa da aka gudanar a Tehran, da kuma samun matsayi na biyu da ba'iraniye ya yi a gasar kur'ani ta kasa da kasa a Malazia ya tabbatar da cewa makaranta Iraniyawa sun yi fice a duniya.

Ya ci gaba da cewa a dukkanin matakai na gasar kur'ani da ake gudanarwa ca duniya Iraniyawa suna taka gagarumar rawa, kama daga bangaren harda da kuma karatun kur'ani da nau'oin kira'a daban-daban, wanda hakan ke nuna irin babban ci gaban da aka samu Iran wajen harkar karatu da hardar kur'ani mai tsarki.

618076




captcha