IQNA

An Kafa Sabuwar Jam'iyar Musulunci A Kasar Faransa

17:57 - July 22, 2010
Lambar Labari: 1960420
Bangaren kasa da kasa; An kafa wata sabuwar jam'iyya ta Musulunci a kasar faransa wadda ta samar da wani sabon shafin sadarwa na yanar gizo domin kara fadada ayyukanta a ciki da wajen kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin ajib cewa, an kafa wata sabuwar jam'iyya ta Musulunci a kasar faransa wadda ta samar da wani sabon shafin sadarwa na yanar gizo domin kara fadada ayyukanta a ciki da wajen kasar ta Faransa.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan jam'iyya tana gudanart da ayyuka na kamfe din addinin Musulunci da kuma muhimmancin shiga cikin harkokin siyasa domin tabbatar da samuwar musulmi a kasar.

Yanzu haka dai jam'iyar tana da wasu ayyukan da take gudanarwa na daban da suka hada kafa ajujuwan koyar da iolmomin addinin Musulunci, ko bayar da fatawoyi da karin bayani kan hukuncin Musulunci.

618884



captcha