Bangaren kasa da kasa; Mahardata kur'ani mai tsarki na kasar Masar na rige-rigen samun damar zuwa gasar karatun kur'ani mai tsarki da aka baiwa taken Makka, wadda za a gudanar a birnin Iskandariyya na kasar ta Masar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na egynews.net cewa, mahardata kur'ani mai tsarki na kasar Masar na rige-rigen samun damar zuwa gasar karatun kur'ani mai tsarki da aka baiwa taken Makka, wadda za a gudanar a birnin Iskandariyya na kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa za a fara gudanar da gasar ne nan da 'yan kawanaki masu zuwa, inda mahardata kur'ani mai tsarki 47 za su kara da juna, wadanda za su fito daga sassa daban-daban na kasar Masar.
Muhammad Wahdan babban sakataren kwamitin kula da harkokin shirya gasar kur'ani na kasa ya bayyana cewa sun kammala dukkanin shirye-shiryen da suka kamata na gudanar da wannan gasa.
618807