Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an muhit an habarta cewa, za a bude tashar talabijin ta farko da za ta rika watsa shirye-shiryenta a cikin harshen isfaniyanci da aka bai wa suna kurtaba wadda za ta fara gudanar da ayyukanta a cikin watan Ramadan.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan tasha za ta mayar da hankali ne wajen watsa shirye-shirye da suka danganci addinin Musulunci, kma da ga saka jawaban malamai, laccoci bayanai na ilimi da dai sauransu.
Tashar za ta rika saka taruka na addini da gasar karatu da hardar kur'ani da ake gudanarwa a kasashen musulmi daban-daban, da kuma wasu daga ayyukan da musulmin kasar Spain suke gudanarwa.
618783