Bangaren kas ada kasa; Za a gudanar da wani taron baje koli a birnin Karbala mai alfarma, da aka bawa taken falala da karamar Imam Hussaein (AS) da za a yi a tsakanin hubbarori biyu masu tsarki da ke birnin.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari day a nakalto daga shafin sadarwa na nun an bayyana cewa, za a gudanar da wani taron baje koli a birnin Karbala mai alfarma, da aka bawa taken falala da karamar Imam Hussaein (AS) da za a yi a tsakanin hubbarori biyu masu tsarki da ke birnin mai alfarma.
Ya kara da cewa daga cikin muhimman abubuwan da za anuna a baje kolin akwai hotuna da kuma fastoci na wuware masu musamman da ke cikin birnin Karbala mai alfarma, da suke alamta wuraren tarihi da ke da dangantaka da ahlul bait (AS) da kuma shi kansa Imam Hussain (AS) musamman.
618760