IQNA

Tafsirin Min Wahyil Kur'ani Khulasar Tunanin Allamah Fadlollah Ne

14:40 - July 24, 2010
Lambar Labari: 1961324
Bangaren kasa da kasa; Sayyid Ali Fadlollah babban da ga marigayi Allamah Fadlollah ya fadi cewa littafin tafsirin nan na minwahyil kur'ani na bayyana tunani da mahangar marigayin ne a kan ilmomin kur'ani da ma'anoninsa.



A wata zantawa da ta hada kamfanin dillancin labaran iqna da Sayyid Ali Fadlollah babban da ga marigayi Allamah Fadlollah ya fadi cewa littafin tafsirin nan na minwahyil kur'ani na bayyana tunani da mahangar marigayin ne a kan ilmomin kur'ani da ma'anoninsa, da ma dalilan safkar ayoyi.

Ya ci gaba da cewa a cikin wannan tafsiri Allamah Fadlollah ya yi amfani da salon a musamman wajen bayyana ilimin tafsirin kur'ani ta hanya mai sauki, ta yadda al'ummar musulmi za ta iya fahimtar ma'anoninsa cikin sauki.

Haka nan kuma a cewar Sayyid Ali mahaifinsa mutum ne mai yin amfani da duk wata dama da ta samu wajen amfanar da jama'a, a kan haka ne ma ya kan yi amfani da ilmin zamantakewa a wajen tafsirin ayoyi masu dangantaka da haka, ta yadda za su yi daidai da zamani da kuma mahallin da musulmi suka samu kansu suna rayuwa.

619847




captcha