IQNA

Allamah Fadlollah Yana Magana Ne Da Mandikin Kur'ani

14:41 - July 24, 2010
Lambar Labari: 1961325
Bangaren kasa da kasa; Marigayi Allamah Sayyid Muhammad Hussain Fadlollah, yana daya daga cikin manyan malaman musulmi masu matukar kaifin hankali da tsabar ilimi, ta yadda ya kan yi magana da wasu masu dauke da wani tunani da mandikin kur'ani.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a gefen taron kasa da kasa da aka gudanar kan Ayatollah Sayyid Muhammad Hussain Fadlollah a birnin Tehran, shugaban cibiyar kusanto da mazhabobin Musulunci Ayatollah Muhammad Ali Tskhiri ya bayyana cewa, marigayi Allamah Sayyid Muhammad Hussain Fadlollah, yana daya daga cikin manyan malaman musulmi masu matukar kaifin hankali da tsabar ilimi, ta yadda ya kan yi magana da wasu masu dauke da wani tunani da mandikin kur'ani mai tsarki.

Ya ci gaba da cewa Sayyid Fadlollah ya kasance daga cikin manyan malaman Musulunci da suke bayar muhimmanci ga tattaunawa tsakanin musulmi da sauran al'ummomi, tare da bayyana musu kyawawan dabi'un Musulunci da koyarwarsa.

Ayatollah Tskhiri ya ce babu wata kalma da za a iya bayyana marigayi Allamah Fadlollah illa a bayyana shi da cewa wani sauti na Musulunci a duniyarmu ta yau, da wanda ambatonsa ba zai taba gushewa ba har karshen duniya.

619824
captcha