IQNA

Tafsirin Fadlollah Min Wahyil Kur'an Na Tartibi Ne

14:41 - July 24, 2010
Lambar Labari: 1961326
Bangaren kasa da kasa; Shaharren tafsirin nan na babban malamin addinin musulunc na kasar Lebanon Ayatollah Sayyid Muhammad Hussain Fadollah tafsiri ne da aka tsara shi a kan hanya ta tartibi.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada shi da daya daga cikin abokan karatun Fadlolah Sayyd Ali Mir Hussain Ashkuwari ya bayyana cewa, shaharren tafsirin nan na babban malamin addinin musulunc na kasar Lebanon Ayatollah Sayyid Muhammad Hussain Fadollah tafsiri ne da aka tsara shi a kan hanya ta tartibi da kuma fayyace bayani.

Malamin ya ci gaba da cewa Allamah Sayyid Muhammad Hussain Fadlollah ya mayar da hankali matuka wajen bayyana addini musulunci a matsayin rayayyen addini, da ya yi daida da kowane irin zamani da mtum zai iya rayuwa a cikinsa.

Y ace Sayyid Fadlollah ya yi rubuce-rubuce masu matukar amfani ga musulmi da ma wadanda ba musulmi ba, ga ma dan adam ga baki daya.

619812



captcha