IQNA

Takurawa DaTakaitawa Yan shi'a A Masar Mataki Na Ruruwa Wuta

15:53 - July 25, 2010
Lambar Labari: 1962045
Bangaren kasa da kasa; matakin baya-bayan nan na jami'an tsaro a Masar na takurawa yan shi'a da hana su yin bulaguro zuwa kasashen Iraki da Iran wani mataki ne na kawo banbanci da wariya a tsakanin musulmin wannan kasa da kuma cinna wutar rikici a tsakanin yan shi'a da sunna na wannan kasar.

Ahmad Halal daya daga cikin shugabannin yan Shi'a a kasar Masar kuma masani kan bincike da rubuce-rubuce a wannan kasa ta Masar a lokacin day a yi wata tattaunawa da cibiyar da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar Musulunci ta Iran Ikna ya bayyana cewa; matakin baya-bayan nan na jami'an tsaro a Masar na takurawa yan shi'a da hana su yin bulaguro zuwa kasashen Iraki da Iran wani mataki ne na kawo banbanci da wariya a tsakanin musulmin wannan kasa da kuma cinna wutar rikici a tsakanin yan shi'a da sunna na wannan kasar. Ya kara da cewa wasu bangarori na tsaro da makamantansu na so ne ta wannna hanya su rura wutar rarrabuwar kawuna a yankin domin cimma burinsu na siyasa a ciki da waje.
619281
captcha