Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar sadarwa ta Rasid ta habarta a shafinta na yanar gizo cewa, 'yan shi'a a kasar Saudiyya za su gudanar da tarukan maulidin Imam Zaman Almahdi (AS) a yankuna daban-daban na kasar da ke da mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah (SAW) musamman a yankunan gabacin kasar.
Bayanin ya kara da cewa mabiya tafarkin iyalan gidan manzo da ke yankunan mabiya mazhabar shi'a a kasar saudiya suna gudanar da irin wadannan taruka a kowace shekara, inda suke gabatar da taruka tare da jawabai, da kuma yin karatun addu'o da suka kebanci wannan lokaci mai albarka.
620223