Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani taron manema labarai da ya gudanar Babban jami'i mai kula da ma'aikatar harkokin addini ta kasar Kuwait ya bayyana cewa ana gudanar da wasu shirye-shirye na zaman taro da zai yi dubi kan matsayin matasa da kur'ani a kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro za a gudanar da shi da nufin kara karfafa gwiwar matasa kan yin riko da koyarwar kur'ani mai tsarki a cikin dukkanin harkokin rayuwarsu.
Walid Shu'aib ya kara da cewa ko shakka babu matasa na da matsayin na musamman a cikin kowace al'umma, bisa la'akari da cewa su ne za a yi alfahari da su a gaba.
621061