Bangaren kasa da kasa; Babban malamin addinin Musulunci nan kuma daya daga cikin jagororin mabiya mazhabar shi'a a kasar Saudiyya Sayyid Hassan Namir ya bayyana cewa, tayar da bama-bamai da ake yi a wuraren ibadar musulmi wani makirci ne na manyan kasashen duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, babban malamin addinin Musulunci nan kuma daya daga cikin jagororin mabiya mazhabar shi'a a kasar Saudiyya Sayyid Hassan Namir ya bayyana cewa, tayar da bama-bamai da ake yi a wuraren ibadar musulmi wani sabon makirci ne na manyan kasashen duniya masu girman kai.
Ya ci gaba da cewa babbar manufar yin hakan ita ce kawo rarraba tasakanin musulmin duniya ta hanayar banbancin mazhaba da ke akwai a tsakaninsu, wanda hakan ne kawai hanyar yin nasara a kansu.
Sayyid ya kara da cewa dole musulmi su zama cikin fadaka dangane da makircin da ake kitsa wa addinin Musulunci da musulmi a kasashen duniya masu girman kai, da nufi raunana karfin musulmi.
621000