Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ic-el an bayyana cewa, za a gudanar da tarukan maulidin Imam Mahdi (AS) a yau a birnin London na kasar Birtaniya, a cibiyar gudanar da harkokin addinin Musulunci da ke birnin na London.
Bayanin ya ci gaba da cewa, taron zai samu halartar masana da malamai na addinin Musulunci daga sassa daban-daban na birnin, domin taya mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (SAW) murnar zagayowar wannan babbar rana mai albarka.
620852