IQNA

Dan Shekaru 8 Da Haihuwa Ya Zo Na Daya A Gasar Harda A Makkah

18:58 - July 26, 2010
Lambar Labari: 1962481
Bangaren kasa da kasa; Wani yaro dan shekaru takwas da haihuwa ya zo na daya a gasar hardar kur'ani mai tsarki da aka gudanar a birnin Makka mai alfarma a kasar Saudiyya, gasar da ta samu halartar mahardata dubu biyu.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga jaridar Almadina an bayyana cewa, wani yaro dan shekaru takwas da haihuwa ya zo na daya a gasar hardar kur'ani mai tsarki da aka gudanar a birnin Makka mai alfarma a kasar Saudiyya, gasar da ta samu halartar mahardata dubu biyu da haihuwa a duniya.

Rahoton ya ci gaba da cewa wannan yaro mai suna Nuwaf Galib ya lashe gasar ne a dukkanin bangarorin hardar kur'ani da kuma tajwidi ba tare da ya yi wani kure ba, wanda hakan ya ba shi damar samun maki 100 daidai ba tare da wani nakasu ba.

Nuwaf Galib ya hardace kur'ani tare da wasu dalibai 800 a birnin Makka mai alfarma, kuma yanzu haka akwai kimanin 1500 da suke cikin hardar, da za su kammala nan bad a jimawa ba.

620883


captcha