IQNA

Ana Gudanar Da Tarukan Maulidin Imam Mahdi (AS) A Malazia

18:56 - July 27, 2010
Lambar Labari: 1962849
Bangaren siyasa da zamantakewa; Ana gudanar da tarukan maulidin Imam Mahdi (AS) a babban dakin gudanar da taruka na birnin Kualalampour na kasar Malazia, wanda ofishin jakadancin jamhuriyar musulunci ta Iran na kasar ya dauki nauyin shiryawa.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Ana gudanar da tarukan maulidin Imam Mahdi (AS) a babban dakin gudanar da taruka na birnin Kualalampour na kasar Malazia, wanda ofishin jakadancin jamhuriyar musulunci ta Iran na kasar ya dauki nauyin shiryawa tare da gudanarwa.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro yana samun halartar Iraniyawa mazauna birnin tare da musulmi daga bangarori daban-daban, musamman ma dai mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah (SAW) da ke kasar.

An gabatar da wakoki na yabon Imam zaman Almahdi (AS) tare da gabatar da jawabai kan matsayin wannan rana da kuma bayanai kan shi kansa Imam Mahdi (AS) wanda aka Haifa a wannan rana.

620972



captcha