Bangaren kasa da kasa; A gobe ne za a fara gudanar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Kualalampour na kasar Malazia a karo na hamsin da biyu, da ake farawa a kowace shekara makonni biyu kafin fara azumin watan Ramadan.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a gobe ne za a fara gudanar kur'ani mai tsarki ta kasa da kasa a birnin Kualalampour na kasar Malazia a karo na hamsin da biyu, da ake farawa a kowace shekara makonni biyu kafin fara azumin watan Ramadan mai alfarma.
Bayanin ya ci gaba da cewa makaranta kur'ani gami da mahardata daga sassa daban-daban na duniya musamman ma ksashen musulmi, za su halarci gasar.
Gasar kur'ani ta kasa da kasa da a kae gudanarwa akasar Malazia tan a daya daga cikin gasar kur'ani ta duniya da aka jima ana gudanarwa a kowace shekara.
A cikin shekara ta 1961 ne aka fara gudanar da wannan gasa a kasar Malazia, wadda tsohon fira ministan kasar Tunko Abdulrahman ya kirkiro a cikin shekarar.
621809