IQNA

Mahangar Imam Khomeini (RA) Abin Koyi Ce Kan Batun Hadin Kai

Bangaren fikira da ilimi; Mabiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah (SAW) suna da babban abin koyi daga mahangar Imam Khomeini(RA) wajen samun hadin kai tsakaninsu, tare da gudanar da ayyuka kan manufa guda daya ta isar da sakon manzo zuwa sauran al'ummar musulmi.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a ci gaba da gudanar da taron mahdawiyya da ake yi a lardin Fars na kasar Iran, daya daga cikin mahalarta taron daga kasar Tunisia, fitaccen malamin nan, kuma malamin jami'a a jami'ar Tunis, marubucin littafin sannan na samu shirya Dokta Tijani Samawi ya bayyana cewa, mbiya tafarkin iyalan gidan manzon Allah (SAW) suna da babban abin koyi daga mahangar Imam Khomeini(RA) wajen samun hadin kai tsakaninsu, tare da gudanar da ayyuka kan manufa guda daya ta isar da sakon manzo zuwa sauran al'ummar musulmi na duniya baki daya.

Malamin ya ci gaba da cewa zamanin yanzu babu abin day a fi dacewa a yi riko da shi wajen samun hadin kan al'ummar musulmi kamar mahangar Imam Khomeni(RA) kamar yadda su ma mabiya mazhabar shi'a bas u da abin ya dace su yi riko da shi wajen samun irin wannan hadin kai tsakaninsu kamar mahangar Imam Khomeini (RA) kan batun hadin kai.

621832