IQNA

Taron Maulidin Imam Mahdi (AS) A Birnin Puna Na Kasar India

18:55 - July 27, 2010
Lambar Labari: 1962853
Bangaren siyasa da zamantakewa; Musulmin birnin Puna na kasar India suna gudanar da tarukan maulidin Imam Mahdi (AS) wanda cibiyoyin musulmin yanki tare da hadin gwiwa da ofishin kula da bunkasa harkokin al'adu na iran da ke birnin Mumbai.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da bangaren hulda da jama'a na karamin ofishin jakadancin Iran da ke birnin Mumbai nakasar Indiya ya bayar, an bayyana cewa msulmin birnin Puna na kasar India suna gudanar da tarukan maulidin Imam Mahdi (AS) wanda cibiyoyin musulmin yanki tare da hadin gwiwa da ofishin kula da bunkasa harkokin al'adu na iran da ke birnin Mumbai fadar harkokin kasuwancin kasar.

Bayanin ya kara da cewa taron yana samun halartar masana gami da malaman addini da kuma malaman jami'a, inda ake gabatar da jawabai da kuma raba makalolin da aka rubuta dangane da wannan rana.

621717


captcha