IQNA

An Gudanar Da Zaman Taron Kan Falsafar Jiran Mahdi A Spain

Bnagaren fikira da ilimi; An gudanar da wani zaman taro a cibiyar bincike ta harkokin al'adu ta Nicolas Salimroz da ke birnin Madrid fadar mulkin kasar Spain, dangane da bahasin falsafar jiran mahdi mai tseratar da duniya.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, An gudanar da wani zaman taro a cibiyar bincike ta harkokin al'adu ta Nicolas Salimroz da ke birnin Madrid fadar mulkin kasar Spain, dangane da bahasin falsafar jiran mahdi mai tseratar da duniya daga duhun jahilci da zalunci da danniya.

Gudanar da wannan zaman taro ya zo a daidai lokacin tunawa da zagayowar ranar haihuwar Imam Mahdi (AS) wanda musulmi suka yi imani da shi, kuma mabiya tafarkin iyalan gidan manzon (SAW) suka yi iamanin cewa an haife a wannan rana.

621732